
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya bayyana cewa ba zai biya diyyar masu hakar ma’adanai 37 da suka rasa rayukansu ba.
Yace ba hakkin Gwamnatin jiha ne ta biya diyyar ba.
Yace masu hakar ma’adanan sun rasu ne a hannun Gwamnatin tarayya dan haka itace zata biya diyyar rayukan.
Rahotanni sun bayyana cewa, Iyayen masu hakar ma’adanan da suka rasa rayukansu, sun nemi Gwamnatin ta biyasu diyyar rayukan ‘ya’yansu.