
Hukumar tattara haraji ta kasa FIRS ta nemi bankuna da su fara kai mata rahoton duk me ajiya da bankunan da ya yi hadahadar kasuwancin data zarta ta Naira Miliyan 5 a wata.
Wannan sabuwar doka zata fara aiki ne nan da shekarar 2026.
Wannan na daga cikin sabuwar dokar Harajin da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa hannu kwanannan.
Hakanan za’a yi amfani da wannan abun domin karfafa biyan Haraji da kuma dakile Almundahanar kudade.
Ana tsammanin duk wata ne bankunan zasu rika baiwa huk ta fIRS wadannan rahotannin.