Friday, January 16
Shadow

Gwamnati ta shiga tsakani a rikicin Dangote da ‘yan kasuwar man fetur da suke zargin Dangoten da yin kaka gida a harkar man fetur

Ministan Kwadago, Muhammadu Dingyadi ya kira Kungiyar ma’aikatan man fetur ta kasa, NUPENG da kuma kamfanin matatar man Dangote dan ya zauna dasu kan rikicin da ya bulla a tsakaninsu.

Kungiyar ta NUPENG ta zargi Dangote da yin kaka gida a harkar man fetur da rashin biyan ma’aikata da kyau da rashin baiwa ma’aikata damar shiga kungiyoyin fafutuka na ma’aikata da sauransu.

Kungiyar Tuni ta shirya shiga yajin aiki dan nuna rashin amincewa da tsare-tsaren Matatar mam fetur ta Dangote wanda tace ya sabawa ka’idar aiki wanda kuma tuni Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince da wannan yajin aiki.

Saidai wannan kira da ministan ya musu ana sa ran dai kawo karshen lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Ahmed Musa ya baiwa Jarumin Kannywood, Jamilu Kochila Gudummawar Naira Miliyan 5 a ranar aurensa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *