Tuesday, March 17
Shadow

GWAMNATI ZA TA BA MAHAJJATA KUƊIN GUZIRINSU A HANNU

Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.

Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ta ce shi ne ya nema wa mahajjatan sauƙin daga Babban Bankin Najeriya CBN.

“An bayyana damuwa game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025,” in ji sanarwar da Stanley Nkwocha ya fitar.

Ta ambato kwamashinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na hukumar alhazai, Aliu Abdulrazaq, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka aikawa matar shugaban kasa, Remi Tinubu da tallafi na murnar zagayowar ranar Haihuwarta, wanda a yanzu kudin sun haura Naira Biliyan 20

“Tun kafin yanzu mun sha yin ganawa game da kuɗin guziri a aikin Hajjin na 2025. Daga baya mataimakin shugaban ƙasa ya shiga lamarin kuma ya nemi alfarmar CBN,” a cewar kwamashinan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *