Gwamnatin jihar Filtao ta bayar da sanarwar dage dokar hana yawo da ta saka tun a watan Janairun wannan shekara a karamar hukumar mulki ta Mangu da kewaye.
Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ne ya saka dokar hana fitan har na tsawon awa ashirin da hudu a kowace rana, bayan wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a kauyukan Punshit da Sabon-Gari inda suka kashe akalla mutum sha uku tare da jikkata karin wasu baya ga kona gidajen jama’a da dama.
Gwamnatin Filaton ta bayyana cewa an saka dokar ne domin a samar da cikakken tsaro da zaman lafiya tsakanin kabilu daban-daban da ke fadin jihar.