
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, Naira Miliyan 1 da Gwamnatin Kano tace a baiwa kowane daga cikin iyala ‘yan Kwallon jihar da suka yi hadari ta yi kadan.
Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace Gwamnatin jihar Kano na da kudin da ya kamata ace abinda zata bayar yafi haka.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da yake aikin hajji, ya ce a baiwa kowane daga cikin iyalan ‘yan kwallon Naira Miliyan 1 sannan a basu kayan abinci kamin ya dawo.