Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Maulidi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana Juma’a 5 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na tunawa da ranar haihuwar annabi Muhammad (S.A.W).

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fitar ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun babbar sakatariya a ma’ikatar, Magdalene Ajani.

Miliyoyin al’ummar Musulmi ne ke bukukuwan Maulidi a Najeriya da kuma faɗin duniya a duk irin wannan lokaci, kowace shekara.

Sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta buƙaci al’ummar ƙasar su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Ana yada rade-radin cewa Rahama Sadau Auren karya ta yi bayan da aka ta kokarin gano wanene mijinta amma abu ya faskara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *