Tuesday, November 18
Shadow

Farashin kayan Masarufi ya sauka a Najeriya>>NBS

Hukumar kididdi ta Najeriya, NBS tace farashin kayan masarufi ya sauka da kaso 22.97 a watan Mayu idan aka kwatanta da na watan Aprilu da yake kaso 23.71 cikin 100.

NBS ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Litinin.

Idan aka kwatanta da shekarar data gabata, farashin kayan masarufin na yanzu yana kan kaso 10.98% ne cikin 100 wanda shima za’a iya cewa ya sauka idan aka kwatantashi dana shekarar 2024 wanda yake akan maki (33.95%).

Yawanci ana tattara farashin kayan abinci ne dana Haya dana ababen hawa wajan fitar da wadannan alkaluma.

Karanta Wannan  Hotuna: Jaruman Kannywood Sun Kaiwa Jagoran Mabiya Shi'a Ziyara Ta Musamman A Gidansa Da Yake Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *