
Gwamnatin tarayya ta dauki manyan lauyoyi ciki hadda tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan Gwamnati, Chief Akin Olujinmi (SAN) dan su kareta game da karar da Gwamnonin PDP 11 suka shigar da ita suna kalubalantar dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Sauran lauyiyin da gwamnatin tarayya ta dauka sun hada da Prof Kanyinsola Ajayi, Jelili Owonikoko, Kehinde Ogunwumiju, Tijani Gazali, Babatunde Obama , Olawale Fapohunda, Olumide Olujinmi, Akinyemi Olujinmi da Ademola Abimbola.
Sauran sune, Akinsola Olujinmi, Oluwole Ilori, Abdulwahab Abayomi, Mojeed Balogun, Jideuche Ezi sai Ramat Tijani.
Gwamnonin jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa ne suka shigar da gwamnatin kara suna neman kotun ta gaya musu ko Shugaban kasa yana da ikon sauke zababben gwamna ya mayeshi da wanda ba’a zaba ba.