Friday, March 6
Shadow

Gwamnatin tarayya ta kasa bayar da umarnin Kotu na tsare malam Sheikh Khalifa Sani Zaria

A yayin da lauyan Malamin Addinin Islama, Sheikh Khalifa Sani Zaria da ake tsare dashi ake zargi da shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki ya shigar da kara kan a saki malamin.

Mai shari’a Justice Peter Lifu ya bukaci lauyan Gwamnati daya kawo takardar kotu data bayar da damar a tsare malamin, saidai Lauyan Gwamnatin ya kasa kawo takardar inda yace a bashi lokaci.

Mai shari’a Justice Peter Lifu ya bayyana bacin ransa sosai akan lamarin inda ya daga ci gaba da sauraren karar zuwa ranar Juma’a.

An dai kama malam ne bisa zargin an aika masa Naira Miliyan 2 na aiki kan yiwa gwamnatin Tinubu juyin Mulki.

Karanta Wannan  Ni Musulmi ne kuma nasa Allah a raina sanda nake aiki, Na yiwa Najeriya aiki tukuru ta yanda ko hutu bana samu, kuma a shirye nake na amsa tambayoyin EFCC, amma dai yanzu basu kamani ba ina nan ina hutawa tukuna>>Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari

Lauyan Malam, Sanusi Musa SAN ya shigar da karar EFCC, DIA, da babban lauyan Gwamnati, da kuma Bankin Ja’iz.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *