
A daren jiyane dai gwamnatin tarayya ta bayyana Usman Nasamu Dakin gari a matsayin jakadan Najeriya a kasar Turkiyya.
Saidai a yau da Safiyar Juma’a, Gwamnatin ta bayyana kwace wannan mukami.
Zuwa yanzu dai ba’a bayyana dalilin Gwamnatin na kwace wannan mukami ba.
Duka sanarwar nadashi da kwace mukamin ta fito ne daga bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga.
Ana tsammanin nan ba da jimawa ba, shugaba Tinubu zai kai ziyara kasar ta Turkiyya.