Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin tarayya ta soke faretin bikin ranar dimokuraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta soke faretin sojoji da ake yi don tunawa da Ranar Dimokuraɗiyya ta shekara-shekara, wadda za a gudanar da bikin ta a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni a matsayin cika shekara 26 da dimokuraɗiyya ta dawo Najeriya.

Bayanan da Kwamitin Harkokin Bikin Ranar Dimokuraɗiyya na Ma’aikatu da dama ya fitar sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar ƙasa baki ɗaya da misalin ƙarfe 7 na safe ranar Alhamis, ba tare da an gudanar da faretin Ranar Dimokuraɗiyya kamar yadda aka saba a baya ba.

Maimaikon faretin, Shugaba Tinubu zai halarci zaman haɗin gwiwa na musamman da za a gudanar a Majalisar Tarayya da ƙarfe 12 na rana.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo:Jama'ar Katsina ku yi Hakuri, kamin in hau mulki na yi Alkawarin duk wata zan rika bada bayanin yawan kudaden da muka samu da yawan wanda muka kashe, amma yanzu da na zama Gwamnan naga abin ba zai yiyu ba>>Inji Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda

Ana sa ran wannan zaman haɗin gwiwa zai ƙunshi jawaban da suka shafi halin da ƙasa ke ciki, tunawa da tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya, da kuma kiran da ake sabunta wa na haɗin kan ƙasa da sauye-sauyen da suka daɗe ana buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *