Sunday, March 16
Shadow

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin a daina cin Ganda

Ministan ci gaban Kiwo, Mukhtar Maiha ya gargadi ‘yan Najeriya da su daina cin Ganda wadda ake yi da fatar dabbobi.

Ministan yace akwai matsalar da cin gandar yakewa jikin dan adam.

Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin samar da mayanka ta zamani wadda kowace sashe na jikin dabbar da aka yanka za’a iya fitar dashi cikin sauki ba tare da wahala ba.

Ya kara da cewa, a jikin dabba babu abin yaddawa.

Ya kara da cewa, a cikin kasafin kudin shekarar 2025 sun ware kudade masu yawa dan samar da gonaki da guraren kiwo na zamani

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Buhari Ya Gwangwaje Mawaƙi Ɗan Soja Da Kyautar Kuɗi Dala Dari A Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *