Friday, January 16
Shadow

Gwamnatin tarayya tace zata rama tsaurara Yin Bizar da kasar Amurka ta kakabawa ‘yan Najeriya

Gwamnatin kasar Amurka tace duk dan Najeriyar dake neman Visa ta shiga kasarta dolene ya nuna yanda yake amfani da kafafen sadarwa na tsawon shekaru 5 baya.

Dokar tace kin yin hakan zai iya sa a hana mutum Visar shiga kasar Amurkar.

Saidai cikin gaggawa, Gwamnatin taraya ta sha Alwashin daukar irin wannan mataki akan ‘yan kasar Amurka masu shigowa Najeriya.

Kasar Amurka ta bayyana wannan sabuwar dokane ta kafar X wanda tace hakan na daga cikin shirin shugaban kasarta, Donald Trump na ganin ya samarwa kasar tasa tsaro.

Me magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Najeriya, Kimiebi Ebienfa ya bayyana cewa, Gwamnatin kasar Amurka tuni ta sanar dasu wannan shiri.

Karanta Wannan  Kamin In Auri Gfresh Har ce min Aka yi Zàrmàlùlùnsà ba ta aiki amma na rufe ido na aureshi, kuma na zauna dashi tun bashi da komai har ya samu budi ya Koma Abuja>>Inji Matar Gfresh Maryam

Yace itama Najeriya zata dauki irin wannan mataki akan ‘yan kasar Amurka masu neman Visa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *