
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara amincewa da batun biyan bashin Naira Tiriliyan 2 na wutar lantarki da akw binta.
Hakan kokarine na samar da ingantacciyar wutar Lantarki a Najeriya.
Na kusa da me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar makamashi, Eriye Onagoruwa ce ta bayyana hakan a wajan wani taron masu ruwa da tsaki na harkar wutar da aka gudanar.
Tace gwanatin na duba muhimmancin hakan wajan samar da wutr Lantarki me karfi. Inda tace gwamnatin na kokarin ganin ta samar da wata hanya ta bashi dan biyan wannan bashi musaman lura da karancin kudin da gwamnatin ke fama dashi.