Wednesday, January 15
Shadow

Gwamnatin Taryya ta bude shafin baiwa kasuwanci masu rijista bashin Naira Miliyan daya dan kara jari, duba yanda zaku yi rijista

Gwamnatin Tarayya ta hannun bankin Bank of Industry ta bude damar baiwa ‘yan kasuwa masu rijista da CAC damar karbar bashin Naira Miliyan 1.

Kasuwanci masu rijista da hukumar CAC ne kawai zasu samu wannan bashi kuma za’a baiwa ‘yan kasuwa miliyan 75 ne wannan bashi inda aka ware Naira Biliyan 75 dan wannan aiki.

Ba’a bukatar ka bayar da collateral ko abinda ake cewa jingina da Hausa kamin ka samu wannan bashi.

Ga wadanda ke son yin rijista ga Link din a kasa:

https://fgnboimsmeinterventionloan.boi.ng/signup

Idan kuma wani dalili yasa ba zaka iya cikewa ba, zamu iya cike maka akan farashi me rahusa.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu: Yanzu muke samun Labarin Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya karbi Katin jam iyyar PDP a mazabarsa dake unguwar Sarki Kaduna

Dan haka sai a tuntubemu akan wannan lamba 09070701569 ga wadanda ke son a cike musu. Amma fa ba kyauta bane.

A jiya,Litinin ne aka kaddamar da wannan sabon shafi inda jami’ar Bankin na Bank of industry Amina Habu Mohammed ta bayyana cewa za’a bayar da wannan bashine dan karfafawa kasuwancin da matsin tattalin arziki ya shafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *