Monday, December 16
Shadow

Gwamnoni sun kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri

Gwamnonin wasu jihohin Najeriya sun ziyarci birnin Maiduguri domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa iftila’in ambaliya da ya auka wa birnin.

Gwamnonin da suka ziyarci Maidugurin sun haɗa da na Legas Babajide Sanwo Olu da na Ondo, Lucky Aiyedatiwa da na Adamawa, Umar Fintiri da kuma na Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq.

Gwmanan Legas – wanda ya bayyana ambaliyar a matsayin mummuna – ya ce gwamnonin sun jajanta wa iyalan mutanen da lamarin ya shafa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

”A matsayinmu na al’umma ɗaya yana da muhimmanci mu haɗa kai don samar da agaji da taimaka wa aikin ceto, tare da tabbatar da cewa waɗanda lamarin ya shafa sun samu tallafin da suke buƙata”, in ji Gwamnan Sanwo Olu.

Karanta Wannan  Ba gaskiya bane Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu basa aiki>>Gwamnatin Jihar Bauchi ta mayarwa da Bankin Duniya martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *