Gwamnan jihar Kano dana Bauchi da kungiyar Dattawan Arewa ta ACF sun nemi gwamnatin tarayya ta saki kananan yara da ake zargi da cin amanar kasa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tuni ya baiwa babban lauyan jihar umarnin daukar mataki akan lamarin.
Hakanan kuma A bangaren gwamnan jihar Bauchi shime ya bayyana takaici da abinda ya faru.
Suma bangaren dattawan Arewa na ACF sun nemi gwamnati data saki yaran da gaggawa sannan kuma ta yi bincike kan tsaresu da aka yi ba bisa ka’ida ba.