
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun kira wani taro na musamman da zai tattauna rikicin dake cikin jam’iyyar da yasa mutane ke ta fita daga cikinta.
Gwamnonin sun kira tsaffin Gwamnonin Jam’iyyar da tsaffin shuwagabannin majalisun tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar dan tattaunawa kan yanda za’a shawo kan wannan matsala.
Jam’iyyar PDP na fama da matsalar ficewar da yawa daga cikin membobinta zuwa jam’iyyar APC me mulki.
Na baya-bayannan sune komawar Gwamnan Jihar Delta,b Sheriff Oborevwori da Tsohon Gwamnan jihar kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa zuwa jam’iyyar APC.
Hakanan duka sanatocin jihar Kebbi su 3 suma sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC da sauransu.