
Wani masani a fannin makamashi kuma me sharhi akan al’amuran yau da kullun, Kelvin Emmanuel ya bayyana cewa gyaran matatun man fetur din Najeriya, Fatakwal, Warri da Kaduna duk yaudarace.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a channels TV.
Hakan na zuwane yayin da sabbin rahotanni ke cewa matatar man Warri da aka ce ta dawo aiki, wata daya ta yi tana aiki ta tsayawa tun watan Janairu da ya gabata.
Matsalar rashin aikin mamatun man fetur din Najeriya matsala ce da ta dade ana fama da ita wadda gwamnatoci da yawa suka kasa shawo kanta.