
Gwamnan babban Bankin Najeriya, Cardoso ya bayyana cewa, Gyare-Gyaren da gwamnatin tarayya ta zo dasu babu sauki amma suna bayar da sakamako me kyau.
Ya bayyana hakane a wajan taron da aka gudanar a birnin Washington DC na kasar Amurka wanda IMF da bankin Duniya suka shirya.
Yace wadannan Gyare-Gyaren sun dora Najeriya a turbar ci gaba kuma a yanzu suna bayar da sakamako me kyau.
Wasu daga cikin Gyare-Gyaren da gwamnatin tarayya ta kawo sune cire tallafin man fetur, cire tallafin dala da sauransu.