Saturday, December 21
Shadow

Hajj 2024: Sarkin Saudiyya ya gayyaci ƴan Najeriya 30 a matsayin baki

Hajj 2024: Sarkin Saudiyya ya gayyaci ƴan Najeriya 30 a matsayin baki

Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz Al Saud, mai kula da Masallatan Harami guda biyu, ya gayyaci ‘yan Najeriya 30 a matsayin baki domin halartar aikin hajjin 2024.

Gayyatar dai ta ta’allaka ne kan irin gudunmawar da mutanen suka bayar wajen fadada ilimin addinin Musulunci da fadakarwa da ake yi a duk shekara yayin ziyarar aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Daga cikin ‘yan Najeriya da aka gayyata akwai kwararre kan harkokin kudi da haraji, Dokta Awa Ibraheem, Grand Khadi na Jihar Kwara, Mai Shari’a Abdullateef Kamaldeen, Grand Khadi mai ritaya, Mai Shari’a Idris Haroun, malamin addinin Musulunci na Jihar Legas, Sheikh Imran Eleha, Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa da Hadiza Ndamadi da Sarauniya Seidat Almubarak, matar Dr Awa Ibraheem.

Karanta Wannan  ALLAHU AKBAR: Ya Rasu A Yau Asabar Bayan An Yi Gama Hawan Arfa Da Shi A Makkah

An kuma mika goron gayyatar sarkin zuwa kasashe casa’in na duniya.

A nata jawabin, Dr Awa Ibraheem, ya nuna matukar godiya ga Sarki Salman bisa karrama shi da wasu da aka yi masa na musamman a matsayin baki zuwa aikin Hajjin bana.

A cewarsa, “Wasu fitattun mutane da suka bayar da gudumawa kuma har yanzu suna bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimin addinin Musulunci da fadakarwa, Sarkin Saudiyya yakan gayyace shi zuwa aikin hajji a matsayin bakonsa”.

A baya dai ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya yi bankwana da maniyyatan Najeriya da suka tashi aikin Hajjin 2024.

Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, ya jaddada sadaukarwar masarautar Saudiyya wajen yi wa alhazai hidima da kuma kula da masu ziyarar dakin Allah mai alfarma.

Karanta Wannan  Ana fama da tsananin zafi a Saudiyya yayin da ake shirye-shiryen fara aikin hajji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *