Wednesday, January 15
Shadow

Hamas ta mayar da martani kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Hamas ta miƙa martaninta game da daftarin tsagaita wuta a Zirin Gaza da Amurka ta gabatar.

Ƙungiyar ta ce ta yi maraba da daftarin mai matakai uku amma kuma tana buƙatar tabbaci daban-daban.

Ciki har da cika alƙawarin dawwamammen zaman lafiya da kuma ficewar dakarun Isra’ila gaba ɗaya daga zirin.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya faɗa tuntuni cewa ba zai dakatar da yaƙin ba har sai sun ga bayan Hamas kwatakwata.

Sakataren harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyara a yankin ya ce alhakin ɗorewar shirin ya dogara amincewar Hamas.

Ƙasashen Qatar da Masar sun bayyana cikin wata sanarwa cewa za a ci gaba da tataunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu.

Karanta Wannan  Tsagaita wuta a Gaza: Ministocin Isra'ila sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin Netanyahu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *