Tuesday, October 15
Shadow

Ba za mu bari a sake kashe lantarki da sunan zanga-zanga ba – ‘Yansandan Najeriya

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari a sake kashe babban layin lantarki na ƙasar ba da sunan zanga-zanga.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a yau Talata ta ce rundunar za ta tura jami’nta domin gadin tashar babban layin mako guda bayan yajin aikin ‘yan ƙwadago ya jefa ƙasar cikin duhu.

Gargaɗin na zuwa ne yayin da rundunar ta ce ta samu labarin wasu na shirin gudanar da zanga-zanga a ƙasa baki ɗaya, tana mai gargaɗin cewa “ba za mu bari a kawo naƙasu ga gine-ginen more rayuwar sauran al’umma ba”.

“Ana tunatar da mutane cewa laifi ne taɓa babban layin wutar lantarki na ƙasa ta hanyar hanawa ko kuma kawo cikas ga samar da wutar,” in ji sanarwar.

Karanta Wannan  Gwamnoni sun kashe Naira Biliyan dari tara da sittin da takwas(968,000,000) wajan Shan kayan zaki da Alawus din taruka a watanni 3 da suka gabata

“Yayin da rundunar ‘yansanda ke da niyyar kare haƙƙin masu son yin zanga-zangar lumana, ba za kuma ta bari a tauye haƙƙin sauran ‘yan ƙasa ba. Ana shawaratar waɗanda ke son yin zanga-zangar lumana su sanar da ‘yansanda domin neman kariyarsu.”

Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka yi na kwana ɗaya kan mafi ƙarancin albashi, wanda ya jawo kashe wutar lantarkin a ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *