Hukumar sojojin Najeriya ta baiwa manyan janarori shinkafa dan a rabawa kananan sojoji.
Saidai Janar Sadiq shi dake kula da sojojin Kano shi yaki rabawa sojojin da yake kula dasu inda ya karkatar da shinkafar.
Cikakken sunan sojan shine General M.A. Sadiq kuma jaridar Daily Nigerian tace yanzu haka yana kulle a Abuja.
An kuma zargi Janar din da sayar da babban janareta dake wajan horar da sojoji na dajin Falgore dake Kano ga masu gwangwan.
Dan haka yanzu an kamashi inda aka mayeshi da Brigadier General A.M. Tukur.
A baya dai akwai sojoji da yawa da suka ajiye aiki saboda zargin rashin kwarin gwiwar yin yaki.
toobit exchange