Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa, An kama wani mutum da muggan makamai a birnin tarayyar.
Mutumin me suna, Obinna Nwigwe An kamashi ne bayan samun bayanan sirri daga Najob Guest House dake Bwari.
A yayin da jami’an tsaro suka je kamashi, an iskeshi ya harbi wani mutum bayan da suka yi gaddama.
Bincike da aka yi sosai a gidansa an gano karin makamai da Albarusai.
wanda ya harba din, Andrew Philemonna can Asibiti yana jinya, a yayin da shi kuma ake bincike akansa.