Friday, November 14
Shadow

Hotuna: Wani muatashi ya kkashe mahaifiyarsa ya jefa gawar a cikin rijiya

Ana zargin wani matashi da kashe mahaifiyarsa sannan ya jefa gawarta a cikin rijiya a Jihar Cross River.

Lamarin ya farune ranar Lahadi a titin Chairman Road, dake garin Ohong karashin karamar hukumar Obudu na jihar.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook, an ga yanda mutanen unguwa suka taru ake zaro gawar matar daga rijiyar da dan nata ya jefata.

Rahotanni sunce wani abokinsa ne ya taimaka masa wajan gudanar da wannan danyen aikin.

Ya yiwa ‘yar aikin gidansu baranar cewa idan ta sake ta gayawa wani sai ya kasheta.

Ya dauki yarinyar aikin gidan nasu akan mashin zuwa wani wajene inda akan hanya ‘yan Bijilante suka taresu, anan ne Asirinsa ya tonu.

Karanta Wannan  Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta gurfanar da tsohon dan majalisa a kotu bisa zargin satar Naira Miliyan 18 inda kotu ta bayar da belinsa akan Naira miliyan 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *