‘Yansanda a jihar sokoto sun kama wani mutum saboda siyar da ‘ya’yansa 6.
Mutumin ya sayar da jimullar kananan yara 28 ciki hadda ‘ya’yan cikinsa 6.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ali Hayatu Kaigama ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kubutar da 21 daga cikin yaran.
Mutumin me suna, Bala Abubakar yana baiwa wasu mata, Kulu Dogon yaro da Elizabeth Ojah yaranne inda su kuma suke bashi Naira dubu dari da hamsin ko kuma Naira dubu dari biyu da hamsin.
Ana cewa wai za’a kaisu Abujane wajan wani mutum da zai rika kula dasu.