Monday, December 16
Shadow

Hotuna da Bidiyo: Kalli Kananan yara da aka barsu da yunwa bayan kamasu saboda sun yiwa gwamnatin Tinubu zanga-zanga, wasu daga cikinsu sun fadi ana tsaka da musu shari’a saboda yunwa, An bayar da belinsu akan Naira Miliyan 10 kowanne yaro daya

Rahotanni daga Babban birnin tarayya Abuja na cewa kananan yara guda 32 ne aka gabatar a gaban babbar kotun tarayyar dake Abuja bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

An kamasu ne saboda sun yi zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Augusta da ya gabata inda tun wancan lokaci suke a tsare.

Jimullar mutane 76 ne ake tsare dasu bisa wannan zargi inda guda 32 kananan yarane.

Saidai a yayin da aka gabatar dasu a kotun an ga mafi yawancinsu suna cikin halin yunwa da rashin lafiya da tashin hankali.

Guda 5 daga cikin yaran sun yanke jiki suka fadi kasa ana tsaka da musu shari’a inda anan lauya ya nemi gwamnati da ta janye zargin da take musu na dan lokaci dan a kaisu Asibiti.

Karanta Wannan  Ba Za Mu Koma Gida Ba Har Sai Taliya Ta Sauko, Vewar Wasu Matasa Masu Źanga-Źànga A Kano

Alkalin Kotun ya amince da wannan bukata inda gwamnati ta dakatar da zargin da takewa yaran 5 da suka fadi kasa kuma aka garzaya dasu asibiti.

https://twitter.com/emmaikumeh/status/1852288015508324755?t=7amEnqY1NvwCq_fNYrzEMw&s=19

Saidai rahotanni sun bayyana cewa da zarar sun warke za’a mayar dasu kotu a ci gaba da musu shari’a.

Su kuwa sauran an bayar da belinsu bisa kowanne daya daga cikinsu sai ya biya Naira miliyan 10 sannan sai ma’ikacin gwamnati dake matakin aiki na 15 ya tsaya musu hakanan dole mahaifin kowane daga cikinsu shima ya je ya tsaya musu.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi Allah wadai da wannan lamari inda da yawa suka nemi a gaggauta sakin yaran ba tare da wani sharadi ba.

Karanta Wannan  Idan Aka raba Najeriya kasar Bìàfrà zan koma da zama inji wannan dan Arewar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *