
Rahotanni daga fadar shugaban kasar Amurka, White House na cewa, shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yin kira ga Firaiministan Israyla Benjamin Netanyahu da a kawo karshen yakin da suke yi da kungiyar Hàmàs.
Trump yace ya damu da hotunan da ya gani na yara suna shan wahala a Gaza yace abin akwai ban tausai.
Yace a yi sulhu sannan a saki wadanda aka yi garkuwa dasu sannan a kawo karshen yakin.
Jaridar Axios ta kasar Amurka tace wasu majiyoyi biyu sun shaida mata hakan daga fadar ta White House.