Mutane akalla 200 ne suka fito a kasar Mexico inda suke nuna rashin jin dadi kan kisan da kasar Israela kewa Falas-dinawa.
Mutanen sun yi arangama da jami’an tsaro inda suka rima jefawa jami’an tsaron duwatsu da wuta da suka kunna a tsumma.
Saidai jami’an tsaron suma sun rika jefawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa da kuma duwatsu.