Thursday, December 25
Shadow

Hukumar EFCC ta kwato jimullar Kudade Naira Biliyan ₦566bn, da Dala Miliyan $411m, da kadarori 1,502 a cikin shekaru biyu

Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kwato kudade akalla Naira Biliyan ₦566bn, da Dala Miliyan $411m, da kadarori guda 1,502.

An samu wadannan nasarorin ne a karkashin shugabancin sabon shugaban hukumar Mr. Ola Olukoyede bayan da ya shafe shekaru 2 yana shugabanci.

Rahotanni sun bayyana cewa, ya fadi hakane ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis a yayin da yake bayar da bayanai kan yanda ya gudanar da ayyukansa a shekaru 2 da suka gabata.

Shugaban EFCC din yace kuma sun sallami ma’aikata guda 55 da aka samu da laifin take doka.

Karanta Wannan  Najeriya na sa ran haƙo gangan ɗanyen mai miliyan1.8 a kullum

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *