
Hukumar yin rijistar katin zama dan kasa ta NIMC ta kara farashin yin katin zama dan kasan.
Tun a ranar 1 ga watan Mayu ne dai hukumar ta NIMC ta sanar da cewa, zata kara farashin yin katin zama dan kasar.
A sanarwar data fitar Ranar Asabar, Hukumar tace ta kara farashin canja ranar Haihuwa daga Naira N16,340 da ake biya a baya, zuwa Naira N28,574 a yanzu.
Hakan na nufin an yi karin kaso 74.87 a cikin kudin.
Farashin canja sauran bayanai kamar suna da adreshin gidan zama shima ya tashi zuwa Naira N2,000 daga Naira N1,522 da ake biya a baya.
Hakan na nufin an samu karin kaso 31.41 cikin 100 akan farashin da aka saba biya.
Bada katin zama dan kasar da rijista duk kyauta ne amma idan ya bace, an canja farashin baiwa mutum sabo daga Naira 500 zuwa 600.