
Hukumar shirya fina-finai ta kasa, NFC ta musanta Bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa dake ikirarin cewa, shugabanta, Ali Nuhu ya mutu.
Jaridar Leadership tace NFC ta gaya mata cewa wannan rashin kyautawa ne da kuma abin Allah wadai inda hukumar ta nemi gwamnati ta saka ido akan kafafen sadarwa da kula da gudanarwarsu.
Daraktan yada labarai na hukumar, Brian Etuk ya bayyana cewa, Ali Nuhu na nan lafiyarsa qalau.
Yace kuma suna nan suna shirin daukar matakin da ya dace kan lamarin.