Friday, December 5
Shadow

Hukumar ‘yansandan Najeriya tace karyane ba’a yi yunkurin shyekye Sojan Ruwa AM. Yerima ba

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na cewa, Hukumar ‘yansandan birnin ta musanta yunkurin kisa da aka ce an yi akan sojan Ruwa, AM. Yerima a daren jiya Lahadi.

Hukumar ‘yansandan ta bakin me magana da yawunta, Josephine Ade tace hankalin hukumar ‘yansandan ya kai kan rahoton cewa an nemi rayuwar AM. Yerima.

Tace wannan ba gaskiya bane, jita-jita ne kawai kuma tace a yi watsi da rahoton.

Rahoton dai yace AM. Yerima na tukine a mota me gilashi me duhu(Tinted) inda har ‘yansanda suka tareshi da neman ya bayyana hakansa, inda yayi, bayan nan ne sai wasu suka rika binsa a baya.

Rahoton dai yace ya samu ya tsere.

Karanta Wannan  Mun ba ɗaliban Najeriya rancen naira biliyan 56.85 a shekara ɗaya - Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *