Thursday, January 9
Shadow

ICPC ta maka tsohon kwamishinan El-Rufai a kotu

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya ICPC ta maka kwamishina a tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi.

Jami’in shari’a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka Bashir Sa’idu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa.

A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohuwar gwamnatin da almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.

Karanta Wannan  Tonon Silili, Kalli Hotuna: An Bayyana 'yan matan kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio har su 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *