Saturday, May 31
Shadow

Idan da gaske kake game da daina Shigo da abubuwa daga kasashen waje a rika Amfani da wanda aka yi a Najeriya, ka ajiye motocin Alfarma da kake hawa ka koma Amfani da motocin Innoson da ake kerawa a jihar Anambra>>Atiku ya gayawa Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu idan da gaske yake maganar daina amfani da abubuwan da aka kera a kasashen waje to ya daina amfani da motocin Alfarmar da yake hawa ya koma Amfani da motar Innoson da ake kerawa a jihar Anambra.

Ya bayyana hakanne bayan da shugaba Tinubu ya baiwa ma’aikatun gwamnati umarnin su daina shigo da kayan da ake yin irin su a Najeriya.

Saidai Atiku yace wannan duk yaudara ce wadda ‘yan Najeriya sun saba ji, yace idan Gwamnatin da gaske take, ta fara daga kan kanta.

Yace kamata yayi shugaba Tinubu ya fara da kanshi, ya daina amfani da motocin Alfarma da yake amfani dasu ya koma amfani da motocin Innoson ko makamantansu da ake kerawa a Najeriya.

Karanta Wannan  Hotuna: Kalli yanda matashi dan fafutuka Khalid ya koma bayan da Hukumar DSS ta sakoshi, an tsareshi tsawon makonni 11 saboda yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kaduna

Yace ministocin Buharin ma haka ya kamata su yi, yace hakanne zai kara karfafa masana’antun Najeriya, ko kuwa Talaka ne kadai zai bi wannan dokar?

Yace hakanan idan da gaske shugaban yake game da karfafa masana’antun Najeriya, kamata yayi ya daina zuwa kasashen Faransa da Ingila dan hutawa, kamata yayi ya rika zuwa wajajen shakatawa na Najeriya ko kuwa bai yadda Najeriyar na da kyau bane?

Atiku ya kara da cewa hakanan idan Shugaba Tinubu da gaske yake ya daina fita kasashen waje neman magani ya rika amfani da Asibitocin Najeriya wajan duba lafiyarsa, idan kuwa ba haka ba to munafurci ne kawai wannan sabon tsarin.

Karanta Wannan  Ka Çìŕè Ģìŕman Ķai Ka Saurari Koken Al'umma Kan Illolin Manufofin Haraji, Sakon Gwamnan Bauchi Ga Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *