Illolin Basir na da yawa ga dukka maza da mata amma a yau zamu yi magana akan illolin basir ga mazane.
Daya daga cikin illolin basir ga maza shine:
Za’a rika jin zafi a dubura.
Kumburi a Dubura.
Kai ka yi a dubura.
Yana da kyau a tuntunbi likita idan aka ji irin wadannan matsaloli ko idan ana tunanin an kamu da cutar Basir.
Ana amfani da hanyoyi da yawa wajan maganin basir kamar su:
Zama akan ruwa me dumi lokaci zuwa lokaci a rana.
Amfani da kankara a dira a wajan dan rage kumburi.
Amfani da man Basir na musamman da ake turawa cikin dubura.
Hakanan ana cin abinci marar tauri dan magance wannan matsala:
Ana iya maida hankali wajan cin abinci irin su:
Kayan marmari.
Ganyayyaki irin su, Alayyahu, Zogale, Kabeji,Latas da sauransu.
Cin abinci me kyau, rage dadewa a bandaki, da kiyaye yin kiba mara misali na taimakawa wajan hana kamuwa da cutar basir.