Thursday, May 22
Shadow

In ka cika Kwallon Shege ka fito mu yi dambe a bainar jama’a a ga wanene gwani ni da kai>>Oshiomhole ya gayawa Reuben Abati

Tsohon shugaban APC, kuma tsohon gwamnan jihar Edo wanda kuma tsohon shugaban kungiyar Kwadago ta NLC ne, watau Adams Oshiomhole ya nemi tsohon kakakin shugaban kasa, Reuben Abati da ya fito su daku idan ya isa.

Ya bayyana hakanne a ganawarsa da gidan Talabijin na Channels TV.

Yace hakane bayan da Abati a wata hira da aka yi dashi a Arise TV ya ce shin ko Ifeanyi Okowa ya tambayi Oshiomhole an yafe masa zunubansa kamin komawa APC?

A baya dai lokacin yana shugaban APC, Adams Oshiomhole ya taba cewa, duk laifin mutum idan ya shiga APC an yafe masa.

Saidai yanzu yace wannan magana da Abati yayi bata dace ba, shi a matsayinsa na Sanata menene hadinsa da binciken me laifi?

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da'awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin

Sannan yace shin ko Abati yana jin haushin kamun da EFCC suka masa ne bayan saukar Jonathan daga Mulki, yace ko kuwa yana jin Haushin rashin nasarar zama mataimakin Gwamnane a jihar Ogun?

Yace da alama dai Abatin na da wata kullalliya tare dashi dan haka ya daina boyewa a gidan TV yana surutai, ya fito su daku a bainar jama’a su kece raini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *