Thursday, June 5
Shadow

Ina gama Wa’adina na Mulki zan koma sana’ar da nake yi kamin in zama Gwamna watau Walda>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi karin haske kan sana’ar da zai fara bayan ya kammala wa’adin mulkinsa zango na biyu.

Gwamna Sule yace zai koma sana’ar da ya fara yi tun kafin fara mulkin jihar Nasarawa wato sana,ar walda, da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027.

Yace akwai alkairi a cikin Sana’ar ta walda sosai ,Inda ya nemi matasa da su dage da Sana’a

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Nasarawa.

Ya kuma yi amfani da damar wajen tabbatarwa da masu sha’awar zuba jari cewa jihar Nasarawa na da ƙwararrun ma’aikata, inda ya nuna cewa jihar na da ɗimbin matasa masu horo da shaidar ƙwarewa da za su iya tallafawa masana’antu.

Karanta Wannan  Kalli Sojar Najeriya data kirkiro Jirgin saman yaki na farko

Gwamnan ya kuma bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin jawo hankalin masu zuba jari zuwa jihar Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *