“A daidai ranar da abokinmu Marigayi Ahmed S Nuhu yake çıka shekaru 18 da komawa ga Mahaliccinmu, ita kuma mahaifiyarsa Allah Ya yı mata rasuwa. Inda za a yi jana’izarta a garin Jos kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Muna addu’ar Allah Ya jikan ta, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya sa Aljanna Madaukakiya ce makomarta. Idan ta mu ta zo kuma Allah Ya sa mu çıka da kyau da İmanı” kamar yadda shugaban hukumar tace finafinai, Abba El-Mustapha ya wallafa.