Sunday, May 25
Shadow

Jarabawar JAMB: Jihohin Anambra da Legas ne suka fi yawan masu satar Jarabawar ta 2025

Rahoton da Hukumar JAMB data fitar ya bayyana cewa, jihohin Anambra da Legas ne suka fi yawan dalibai da ake zargi da aikata satar jarrabawar UTME na shekarar 2025, inda aka kama mutane 80 ta hannun ‘yan sanda.


Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Abuja, ranar Juma’a.

Ya ce an gano sababbin hanyoyin satar amsa, ciki har da canjin fasalin fuska da yatsun hannu tsakanin ɗalibai da masu yi musu jarrabawa a madadinsu, tare da hadin gwiwar wasu cibiyoyin CBT.


Anambra ce ke kan gaba da mutum 14 da ake zargi, inda 13 daga ciki ke fuskantar tuhuma kan amfani da wasu wajen rubuta musu jarrabawa, sannan guda ɗaya na da matsalar daidaito hoton wani da bayanan yatsa.

Karanta Wannan  Ni ba irin sakarkarun 'yan siyasar nan bane wanda kawai daga an musu zargin karya sai su sauka daga mukaminsu, Ni ba zan sauka daga kan mukami na ba>>Godswill Akpabio


A jihar Legas, an kama mutum tara bisa zargin amfani da waya yayin jarrabawa, satar amsa, da kuma yin jarrabawa a madadin wasu.


Sauran jihohin da aka fi kama mutane

  • Delta – mutane 8 kan laifin musanya
  • Kano – mutane 7 kan musanya da amfani da waya
  • Kaduna – mutane 6 kan laifin satar amsa da waya
  • Rivers – mutane 6, ciki har da wadanda aka kama da kalkuleta
  • Ebonyi da Enugu – mutane 5 kowanne kan zargin musanya
    A cewar JAMB, daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zauna jarrabawar UTME ta 2025, fiye da miliyan 1.5 sun kasa samun maki 200, wanda shi ne matsakaicin ma’auni na cin jarrabawa. UTME na cikin maki 400 gaba daya, kuma “Use of English” na wajibi ne ga kowa, sai sauran fanoni uku na zabi.
Karanta Wannan  Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *