Wednesday, January 15
Shadow

Ji abinda Bello Turji yawa mutanen Moriki a jihar Zamfara da ya tayar da hankula

Shugaban ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane, Bello Turji ya nemi mutanen garin Moriki dake jihar Zamfara su biyashi Naira Miliyan 50 a matsayin diyya.

Saidai an yi tattaunawa mutanen sun yadda zasu biyashi Naira Miliyan 30.

Wadannan kudade suna a matsayin diyyar shanun Bello Turji ne da sabon shugaban sojoji na harin Morikin yayi inda Bellon yace idan ba’a biyashi ba zai kai hari garin.

Shahararren dan jarida, Bulama Bukarti ne ya bayyana hakan inda yace shugaban sojojin ya nemi mutane kada su biya kudin amma basu saurareshi ba dan sun san Bello Turji zai iya kai musu hari.

Kowane gida suna biyan Naira 10,000 sai kuma wanda bashi da aure yana biyan Naira dubu 2.

Karanta Wannan  Tarewar Ƙaramin Ministan Tsaro Jihar Sokoto Shin Ko Kwalliya Ta Fara Biyan Kuɗin Sabulu Cikin Yaƙi Da Ƴaɲ Tá'aḍdą ?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *