Wednesday, October 9
Shadow

Maganin mura mai toshe hanci

Akwai magungunan mura na gargajiya dana bature da suke aiki sosai ga masu fana da mura.

A wannan bayani zamu fadi magungunan da ake amfani dasu suka inganta daga wajan masana kiwon lafiya.

Idan ana fama da mura, musamman wadda ta toshe hanci, ana son mutum ya yawaita shan abu me ruwa-ruwa.

Ana kuma son mutum idan da hali ya sha farfesun kaza wanda ke da dan yaji, hakan na taimakawa sosai.

Idan kuma makogoro na kaikai, a dumama ruwa da gishiri a barshi ya huce amma da dan dumi a rika wasa sashi a makogoron.

Hakanan likitoci sun tabbatar da cewa tsotsar kankara ta ruwan sanyi, musamman wadda babu sugar/sikari a ciki tana maganin kaikayin makogoro sosai, ko da kuwa kaikayin makogoron ya kai matakin da da kyar ake shan ruwa.

Hakanan Lemon Grass wadda tana fitowa a wasu gurare ko kuma ana samunta a kasuwa wajan musamman maau sayar da citta da kanunfari itama tana maganin kaikayin makogoro sosai idan aka yi shayinta, ana iya hadawa da zuma dan samun dandano.

Hakanan Lemin tsami na maganin toshewar hanci sosai,kamin a kwanta ana iya dafashi a sha, insha Allah za’a tashi da sauki.

Idan Hanci ya toshe dalilin Mura, ana iya tashi a motsa jiki ta hanyar gudu, ko tafiya da sauri-sauri ko aikace-aikacen cikin gida da dai sauran hanyoyin motsa jiki,hakan na taimakawa hanci ya bude idan ya toshe.

Hakanan ana iya hada ruwa da gishiri a rika kwararawa a hanci a rika fyacewa, wannan ma yana bude hanci idan ya toshe dalilin mura.

Allah ya kara sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *