Friday, December 5
Shadow

Ji Dalilin da yasa Kasar Saudiyya ta hana Sheikh Dr. Ahmad Gumi yin aikin Hajjin bana, kamar yanda yayi karin bayani

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana babban malamin addinnin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin hajjin bana.

Sheikh Gumi wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnatin Saudiyya bayan ta ba shi bizar shiga ƙasar domin aikin Hajji amma kuma sai ba a ba shi damar shiga Madina domin fara aikin ibada ba.

“Bisa waɗansu dalilai saboda ra’ayi na kan siyasar duniya, hukumomi a Saudiyya ba sa son kasancewata a Hajji duk da sun ba ni biza,” in ji Sheikh Gumi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya ƙara da cewa “Ina godiya ga hukumomi a Najeriya waɗanda suka sha alwashin tuntuɓar hukumomin Saudiyya a kan wannan lamarin.”

Karanta Wannan  ALLAH SARKI: Aishat Aliyu Mamancy Ta Bar Wasiyya Cewa "Ina Roko Duk Ranar Da Labarin Mutuwata Ya Riske Ku, Don Allah Ku Roka Min Rahamar Ubangiji"

Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na cikin tawagar malaman da hukumar aikin hajjin Najeriya – NAHCON ta ɗauki nauyi domin zuwa aikin ibada a Saudiyya.

Gumi ya isa Madina ne tare da sauran malamai a ranar Asabar ɗin da ta gabata da misalin karfe 10:30 na dare a cikin jirgin sama na kamfani Umza Air, amma da isarsu filin jirgin sama na birnin sai jami’an hukumar shige da fice na Saudiyya suka hana malamin shiga cikin ƙasar.

Bayanai sun nuna cewa a yanzu haka Sheikh Gumi ya koma Najeriya domin ci gaba da harkokinsa na yau da kullum musamman karantarwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Buhari ya koma gidansa na Kaduna da zama bayan kwashe kusan shekaru 2 a Daura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *