Thursday, December 25
Shadow

Ji irin Wilakancin da Inyamuray sukawa El-Rufai a Jihar Imo, sun ce yanda bayya sonsu suma basa sonsa

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kai ziyara jihar Imo tare sa Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Watau Peter Obi.

Sun je halartar wani taron bita da aka shirya ne a birnin Owerri na jihar ta Imo ranar Asabar.

Saidai sun fuskanci zanga-zanga inda iyamurai da yawa suka taru suka ce El-Rufai ba zai shiga dakin taron ba saboda irin abinda yawa Kiristoci a lokacin da yayi gwamnan jihar Kaduna.

Sun kuma ce Peter Obi ya ci amanarsu kuma sun daina goyon bayansa tunda ya kawo musu makiyinsu jiharsu.

Rahoton yace masu zanga-zangar inyamurai sun rika daga kwalaye masu dauke da rubutun cewa kai ma Peter Obi ka zama makiyin mu kuma mutuncinka ya zube a idonmu saboda kawo mana El-Rufai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wata baturiya ta lalata Talabijin dinta saboda bata ji dadin harin da Israyla ta kaiwa kasar Ìràn ba

Rahoton yace jami’an tsaro sun so murkushe masu zanga-zangar amma abu ya faskara.

Rahotanni daga kafar Daily Post ya kuma ce dole jami’an tsaro suka samu da kyar suka fitar da El-Rufai daga wajan taron zuwa wani guri dan tsaron lafiyarsa.

Yayin da shi kuma Peter Obi masu zanga-zangar suka ci gaba da yi masa ihun bama so

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *