Wednesday, January 15
Shadow

Ji Sautin Murya dake alamta cewa Hukumar ‘yansanda ta jihar Kano ce ta kama yarannan da aka kai Kotu a Abuja sannan kuma Gwamnatin jihar Kano ma tasan da maganar

Wani sautin muryar Rahoton BBC ya bayyana da ya ruwaito kakakin ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa na cewa sun kama mutane 76 sun kaisu Abuja saboda cin amanar kasa ta hanyar daga tutar kasar Rasha yayin zanga-zangar yunwa.

Idan dai ba’a manta ba, jimullar mutanen da aka kai kotu ranar Juma’ar data gabata 76 wanda daga cikinsu 32 kananan yara ne.

Hakanan a cikin Rahoton na BBCHausa an ji muryar kwamishinan Shari’a na jihar Kano yana tabbatar da cewa suna sane da kama wadannan yara.

https://twitter.com/jarmari01/status/1852792794475061401?t=oLLGzdsy6cc-uFDh2TMihQ&s=19

Lamarin gurfanar da wadannan yara a gaban kotu dai ya dauki hankula a ciki da wajen Najeriya inda akaita Allah wadai.

Karanta Wannan  Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Zuwa yanzu dai Babban Lauyan gwamnati ya karbi maganar shari’ar yaran kuma ana tsammanin gwamnati zata yafe musu laifin cin amanar kasa da ake zarginsu dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *