Rahotanni sun bayyana cewa, jam’iyyun Hamayya a Najeriya sun samu karfin gwiwar kayar da Gwamnati me ci ta Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027 idan Allah ya kaimu.
Sun samu wannan kwarin gwiwar ne bayan da suka ga jam’iyyun adawa a kasashen Amurka da Ghana sun yi nasara akan jam’yya me mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 26 ga watan Nuwamba, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Peter Obi sun yi tattaunawa inda suka yanke shawarar hada kai dan kafa sabuwar jam’iyya ko kuma shiga wata dan su kayar da Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027.
Hakanan a ranar 30 ga watan Nuwamba ma Atiku da Peter Obi sun sake tattaunawa a Adamawa.
Kakakin Atikun, Paul Ibe ya tabbatar da cewa, me gidansa, Atiku Abubakar ya janyo hankalin jam’iyyun hamayya da su hada kai dan kayar da gwamnatin Tinubu a zaben shekarar 2027 saboda gazawarta, ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV ranar 10 ga watan Disamba.
Ya kuma tabbatar da cewa manyan jagororin adawar na ci gaba da tattaunawa da juna akan wannan aniya tasu.