Bayan hukuncin kotu kan rushe sabbin masarautun Kano, lamarin ya jawo cece-kuce a jihar inda mahawara ta yi zafi kuma kowane bangare tsakanin gwamnatin Kano, da Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero ke ikirarin yin nasara, Gwamnatin jihar ta sa a rushe gidan sarki na Nasarawa wanda sarki Aminu ke ciki.
A wasu hotuna da bidiyo da suka watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda motocin rushe gida suka je fadar ta Nasarawa.
Yayin da yake mayar da martani akan wannan lamari, dan gidan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi ya bayyana cewa:
“Me Ke faruwa ina bacci kuma”
Wani ya tambayeshi
“Wai Bacci ka yi?”
Shi kuma ya amsa da cewa, “Likimo na yi”
Da yawa dai sun fassara Kalmar Likimo da Ashraf yayi amfani da ita a matsayin tsokanar tsohon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda shine shugaban jam’iyyar APC a yanzu wanda kuma wasu majiyoyin ke raderadin yana da alaka da dambarwar sarautar Kano dake faruwa yanzu haka.
Kalmar Likimo dai ta yi suna sosai a tsakanin Hausawa bayan da Gwamna Ganduje ya taba amfani da ita yayin da yake mayar da martani akan masu cewa yana bacci a bainar Jama’a.
Yace likimo yake yi amma yana sauraren duk abinda ake.