
An kai Uwargida da Amarya Asibiti bayan da suka sha maganin kayan mata dan su burge mijin su.
Lamarin ya farune a garin Dakwa dake yankin Bwari na babban birnin tarayya, Abuja.
Sun sha wannan maganin ne bayan da mijinsu yayi sabuwar Amarya dan su ma ya ji su zanzan.
Mijin ya je jiharsa ta Zamfara inda ya karo auren mata ta 3.
Da yake gayawa manema labarai yanda lamarin ya faru, mijin me suna Musa Muhammad yace yana dayan gidansa sai aka kirashi aka ce matansa sun kwanta basu da lafiya.
Yace da ya je sai ya gansu suna ta birgima a kasa cikinsu na ciwo, yace da farko ya kira wata Nurse ce dan ta dubasu, inda ta saka musu karin ruwa.
Yace amma abin yaki ci yaki cinyewa, dole aka kaisu Asibitin madalla inda likitoci suka ce maganin matan da suka sha ne har ya fara lalata musu wasu abubuwa a cikinsu.
Yace an musu aiki an sallamesu.
Yace ita kuma wadda ta sayar musu da maganin kayan matan ana neman ta dan a gudanar da bincike dan kuma baiwa sauran mutane kariya.